Man Utd ta doke Bayern Munich a China

Wasu masu sha'awar kungiyar Manchester United kenan a China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rahoton ya ce ziyarar da Manchester United ta kai China a shekarar da ta wuce ta yi tasiri wajen kara mata farin jinin

Manchester United ta maye gurbin Bayern Munich a matsayin kungiyar da ta fi farin jini a shafukan intanet a China, kamar yadda wani sabon rahoto ya nuna.

Rahoton da ake kira 'Red Card', na karo na shida, wanda ke nazarin tasirin kungiyoyin kwallon kafa na Turai 53 a shafukan sada zumunta na intanet, na China ya nuna Arsenal da Liverpool a matsayin na uku, inda Manchester City ta ke matsayi na biyar.

Gasar Bundesliga ta Jamus ta ci gaba da kasancewa mafi farin jini da tasiri a wurin masu ziyarar shafukan intanet din na China.

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil shi ne na biyu a farin jin bayan dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo.

Dan wasan Manchester United na gaba Wayne Rooney, wanda ake maganar cewa zai koma China, shi ma ya kasance cikin 'yan wasa biyar da suka fi farin jini a shafukan na intanet na China, tare da abokin wasansa a Old Trafford Anthony Martial.

Dan wasan Real Madrid kuma na yankin Wales Gareth Bale, shi ne na uku, amma kuma abin mamaki ba Lionel Messi a cikin jerin, domin dan wasan na gaba na Barcelona ba shi da farin jini a shafukan sada zumunta na intanet a China.

Rahoton ya tattara bayanansa ne daga shafukan sada zumunta na intanet na China, na WeChat da Weibo, da alkaluman masu wasannin kwanfuta na kungiyoyi da kuma yadda ake ziyarar shafukan intanet na kungiyoyin kwallon kafar Turan a China.

Ga yadda jerin kungiyoyin da suka fi farin jinin yake:

1- Manchester United

2- Bayern Munich

3- Arsenal

3- Liverpool

5- Manchester City

6- Real Madrid

7- AC Milan

8- Tottenham

9- Borussia Dortmund

10- Barcelona