Boksin: Haye na bukatar shinge tsakaninsa da Bellew

Haye da Bellew na nemn dambatawa

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Haye (daga haguleft) ya kai wa Bellew naushi bayan da Bellew ya ture shi

David Haye ya bukaci da a sanya wani makari tsakaninsa da abokin karawarsa na kambin ajin masu nauyi na damben boksin Tony Bellew, kafin ranar dambensu na birnin Landan ranar 4 ga watan Maris.

'Yan damben sun yi ce-ce-ku-ce, kafin karon-battar nasu n filin O2 Arena, kuma a mako mai zuwa ne za su halarci wani taron manema labarai, kan damben.

A kan bayyanar da za su yi gaban 'yan jaridun ne, Haye mai shekara 36 ya ce akwai bukatar a gindaya wani shinge tsakaninsu, na gilas ko wani abu, amma dai ba mutane ba, domin mutane ba za su isa hana su ba wa hammata iska ba.

A wani taron manema labarai da suka yi a watan Nuwamba, Haye ya kai wa Bellew naushi, bayan da shi Bellew din ya kalubalance shi a bainar jama'a a watan Oktoba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yi dauki-ba-dadi a taron manema labarai da 'yan damben suka yi a watan Nuwamba

Haye ya kai wannan naushi ne kusan shekara biyar kenan bayan da ya ba wa hammata iska da Dereck Chisora a wani taron manema labarai, kuma shekara shida bayan da Bellew mai shekara 34 ya kicime da Nathan Cleverly a wani taron 'yan jarida, har sai da aka shiga tsakaninsu.

Bellew zakaran duniya mai rike da kambin matsakaita nauyi na WBC, zai fafata a ajin masu nauyi kenan a karon farko, abin da ke nufin zai kammala cirawa daga ajin nauyi biyu, bayan da ya fafata a ajin marassa nauyi a 2013.

A damben da ya yi 31, ya yi nasara a 28, da kuma canjaras a guda daya, inda shi ma Haye, wanda ya dawo fagen boksin a 2016, bayan ya yi ritaya sama da shekara uku, yake bugun kirji da nasara sau 28 a karawa 30 da ya yi.