Boksin: Amir Khan na tattaunawa da Pacquiao

Amir Khan da Manny Pacquiao

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A 2015 Khan ya ce shi ne aka tsara zai kara da Pacquiao, amma na daurin ba ya son dambatawa da shi

Dan damben boksin na Birtaniya Amir Khan yana tattaunawa da Manny Pacquiao domin zama abokin karawa na gaba na zakaran damben na duniya na ajin matsakaita nauyi na WBO, kamar yadda 'yan damben biyu suka bayyana.

A makon da ya wuce ne Pacquiao ya bukaci mabiyansa na shafin Twitter su zaba masa, abokin karawarsa na gaba, inda suka zabi khan mai shekara 30.

Khan ya yi nasarar samun wannan dama ne da kashi 48 cikin dari, a kan dan uwansa dan Birtaniya Kell Brook da dan Australiya Jeff Horn da Ba'amurke Terence Crawford.

A sanarwar da ya yi ta shafinsa na Twitter, Pacquiao dan Philippines, ya ce, suna cikin tattaunawa akan maganar a yanzu.

Pacquaio, mai shekara 38 wanda zakaran aji-aji har shida ne a damben boksin, ya ce zai yi dambensa na gaba ne a Hadaddiyar Daular Larabawa.

A watan Afrilu ne ya yi ritaya daga boksin, amma kuma ya sake dawowa ruwa ya karbe kambinsa na ajin matsakaita nauyi bayan ya doke Jessie Vargas a watan Nuwamba.