Wakilin Rooney ya tafi China neman kungiya

Wayne Rooney

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wayne Rooney shi ne dan wasan da ya fi ci wa Manchester United kwallo

Wakilin Wayne Rooney Paul Stretford ya je China domin ganin ko zai kulla wata yarjejeniya da wata kungiya da za ta sayi dan wasan na gaba ya bar Manchester United.

Sai dai kuma wasu rahotanni na nuna cewa, babu tabbas cewa eja din zai yi nasara a tattakin, wanda ya sa ake ganin da wuya a cimma wata yarjejeniya kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta China ranar Talata 28 ga watan Fabrairu.

To amma tafiyar ta Stretford zuwa China alama ce karara da ke nuna cewa kocin United Jose Mourinho zai bar Rooney, mai shekara 31 ya tafi.

Kuma idan har kyaftin din na Ingila bai tafi ba a wannan watan, bisa ga dukkan alamu zai bar kungiyar a bazara.

Wasu kungiyoyin China sun dade suna nuna sha'awarsu da dan wasan, ko da yake ba a san kungiyoyin da Stretford ya tattauna da su ba.

Sai dai kuma biyu daga cikin kungiyoyi ukun da ake ganin za su sayi dan wasan sun ce ba su da bukatarsa.

A ranar Talata Mourinho ya ce bai san ko Rooneyn wanda ya dawo atisaye kwanan nan bayan jinyar raunin da ya yi na cinya, zai kasance a kungiyar ba nan da mako daya.

Haka kuma ba a san ko wannan halin da ake ciki game da dan wasan ba, zai shafi damar sa shi a wasan karshe da Man United za ta yi da Southampton na kofin Lig (EFL) ranar Lahadi 26 ga watan nan na Fabrairu a Wembley.