Ina nan daram a Man United—Rooney

Wayne Rooney
Bayanan hoto,

Wayne Rooney shi ne kuma ya fi ci wa Ingila kwallo a tarihi, inda ya ci 53 a wasa 119

Kyaftin din Ingila Wayne Rooney ya ce yana nan daram a Manchester United, ba inda za shi, bayan rahotannin da ke cewa zai koma China.

Dan wasan mai shekara 31 ya ce yana ma fatan zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a sauran wasannin kakar Premier ta bana.

Rooney wanda ya ce ya ji dadin kasancewa a kungiyar sannan yana son ci gaba da zama da ita, ya kara da cewa duk da sha'awarsa da wasu kungiyoyi ke yi, abin da ya ce ya gode, yana son ya kawo karshen rade radin da ake yi, ya tabbatar da cewa yana nan a Manchester United.

Rooney wanda shi ne dan wasan da ya fi ci wa United kwallo a tarihi, ya dauki kofin Premier 5 da na Zakarun Turai, tun lokacin da ya koma kungiyar yana shekara 18, a kan fan miliyan 27, daga Everton a 2004.

Dan wasan na gaba wanda kwantiraginsa zai kare a 2019, ya ce ba zai yi wasa a wata kungiya ta Ingila ba, bayan United ko Everton.

Man United ita ce ta shida a teburin Premier. Kuma tana cikin gasar Kofuna uku, bayan da ta kai matakin kungiyoyi 16 na Kofin Turai na Europa ranar Laraba.

Kungiyar za ta kara da Southampton a wasan karshe na kofin Lig (EFL), ranar Lahadi, kafin kuma ta fafata da Chelsea a wasan dab da na kusa da karshe na kofin FA, ranar 13 ga watan Maris.