An ci tarar Celtic euro 19,000 kan rikicin Man City

A yayin wasan ne magoya bayan kungiyoyin suka yi fada da juna

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A yayin wasan ne magoya bayan kungiyoyin suka yi fada da juna

Hukumar kwallon kafar Uefa ta ci tarar kungiyar Celtic euro 19,000, kan hayaniyar 'yan kwallo da kuma wasan wuta, a lokacin wani wasa na gasar zakarun Turai da suka yi da Manchester City, a watan Disambar bara.

Uefa tana tuhumar Celtic da janyo rikici a wasan da aka tashi canjaras 1-1 a filin wasa na Etihad a Manchester City.

Wannan ne karo na 10 cikin shekara biyar da ta gabata, da hukumar Uefa ta tuhumi kungiyar Celtic, kan rashin da'ar magoya bayanta.

Canjaras din da suka yi a wasan ya sa Celtic ta koma can kasa a teburin gasar.

Kawo yanzu dai kungiyar ta Celtic ba ta ce komai ba a kan tarar da aka yanka mata din.