Tottenham ta doke Stoke 4-0, ta zama ta biyu a tebur

Harry Kane
Bayanan hoto,

Yanzu Harry Kane ya ci wa Tottenham kwallo 22 a bana, bayan ukun da ya zura wa Stoke

Tottenham ta huce haushin fitar da ita daga gasar Kofin Europa,a kan Stoke, inda ta zazzaga mata kwallo 4-0, ta zama ta biyu a teburin Premier.

Harry Kane ne ya ci kwallo uku a cikin minti 23 kafin tafiya hutun rabin lokaci, wanda wannan shi ne karo na tara da yake cin kwallo uku-uku a gasar.

Dan wasan ya ci kwallon farko a minti na 14, ya kara ta biyu a minti na 32, sannan kuma ya kara ta uku bayan minti biyar.

Dele Alli ne ya kara ta hudu a ragar bakin, ana daf da tafiya hutun rabin lokacin.

In ban da dan wasan bayanta Toby Alderweireld, wanda ya ji rauni, Tottenham ta ji dadin wasan, wanda ya zamar mata kamar huce haushin fitar da ita da Gent ta yi ranar Alhamis daga gasar Turai ta Kofin Europa.

Da wannan sakamakon yanzu Tottenham ta wuce Manchester City, inda ta zama ta biyu da maki 53 a wasa 26, amma da tazarar maki 10 tsakaninta da Chelsea ta daya a tebur.

Manchester City tana matsayi na uku da maki 52, amma kuma da kwantan wasanta daya da Manchester United, wanda aka daga saboda United din za ta yi wasan karshe na kofin llig (EFL), da Southampton.