Leicester : O'Neill ya kawar da yuwuwar maye gurbin Ranieri

Claudio Ranieri Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kori Ranieri Leicester na maki daya tsakaninta da rukunin faduwa daga Premier

Tsohon kocin Leicester Martin O'Neill ya kawar da yuwuwar maye gurbin Claudio Ranieri a matsayin kocin kungiyar, kuma ya soki tasirin da 'yan wasa suke da shi a wasan kwallon kafa a yanzu.

O'Neill, mai shekara 64, ya ce 'yan wasan gasar Premier suna da tasiri da karfi da iko sosai, wanda, wannan yana shafar wasan kwallon kafa.

BBC ta fahimci cewa an gayyaci wasu 'yan wasan Leicester su gana da shugaban kungiyar, bayan da Sevilla ta doke su 2-1 a gasar Kofin Zakarun Turai ranar Laraba, kuma daga bayanan da suka bayar ne aka kori kocin.

A hirarsa da BBC tsohon kocin ya ce, shi bai ga dalilin da zai sa a ce, a yau kuma a wannan zamanin, 'yan wasa za su je su gana da masu kungiyar wasansu ba.

Sai dai ma'aikata da 'yan wasan kungiyar sun musunta cewa, sun yi wa kocin dan Italiya, wanda aka kora ranar Alhamis, tawaye ko sun juya masa baya.

Mai tsaron ragar kungiyar Kasper Schmeichel da dan wasan gaba Jamie Vardy sun musanta zargin da ake yi musu cewa sun yi kokarin ganin an kori kocin, wata tara bayan ya daukar musu Kofin Premier.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption O'Neill tare da Matt Elliott lokacin da Leicester ta dauki kofin lig a 2000, wanda kuma ta sake dauka a 1997

O'Neill ya yi wa Leicester koci tsawon shekara biyar tsakanin 1995 da 2000, inda ya kai ta gasar Premier tare da daukar kofin lig (EFL) sau biyu.

Tsohon kocin na Aston Villa da Celtic wanda ya ce ba zai koma aikin horar da Leicester din ba, ya ce ya fi son ya ci gaba da aikinsa na jagorantar tawagar Ireland domin ya kai ta gasar cin Kofin Duniya.

Ya ce yana jin dadin aikinsa na kocin kasa maimakon wata kungiya, kuma ya ce yana da aikin da yake gabansa a yanzu