Barcelona ta zama ta daya a tebur

Lionel Messi lokacin da ya ci Atletico Madrid
Bayanan hoto,

Kwallo 22 kenan Messi ya zura a ragar Atletico a gasar La Liga

Barcelona ta hau kan teburin La Liga da maki 54 bayan da ta bi Atletico Madrid gida ta doke ta da ci 2-1, sai dai Real Madrid ka iya dawowa matsayin idan ta yi nasara a wasanta da Villareal.

Rafinha ne ya fara ci wa Barca kwallo a minti na 64, kafin Diego Godin ya farke, minti shida tsakani.

Sai dai an kusa tashi daga wasan ne a minti na 86 sai Lionel Messi ya ci kwallon da ta ba Zakarun na La Liga nasara.

Amma kuma Real Madrid, wadda take da kwantan wasa biyu za ta koma kan teburin, idan ta yi nasara a wasanta da Villarreal yau Lahadi da karfe 8:45 agogon Najeriya.

Yanzu Atletico, wadda ta dauki kofin na La Liga a shekarar 2014, tana matsayi na hudu da maki 45, tara kenan tsakaninta da ta daya.

Kwallon da Messi ya ci, ita ce ta 20 da ya jefa a wasa 21 da ya yi na La Liga a bana.

Haka kuma ita ce ta 21 da ya jefa ragar kungiyar Atletico Madrid a gasar La Liga.

Yanzu dai za a iya cewa fatan Atletico na daukar kofin bana na gasar ya kare, amma kuma wasa takwas ba tare da an ci ta ba, ciki har da nasara shida, abu ne da ya ba su kwarin guiwa.

Abin tambaya a nan yanzu shi ne ko Atletico za ta iya tsira da matsayin gurbin zuwa gasar kofin Zakarun Turai, yayin da ta biyar a tebur Real Sociedad ke bayanta da maki daya?

Ga sakamakon sauran wasannin La Liga da aka yi na ranar Lahadi 26 ga watan na Fabrairu

Espanyol 3 - 0 Osasuna

Athletic Club 3 - 1 Granada

Sporting Gijón 1 - 1 Celta de Vigo