Man Utd ta dauki Kofin Lig, bayan ta doke Southampton 3-2

Ibrahimovic a lokacin da ya kai kora gidan Southampton Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sau biyar kenan Manchester United ta dauki Kofin Lig

Manchester United ta dauki kofin lig na Ingila (EFL) bayan da ta doke Southampton 3-2, a filin wasa na Wembley, ranar Lahadi.

Kwallon da Ibrahimovic ya ci a minti na 87, ita ba su damar daukar kofin, aka ta shi 3-2.

Tun da farko dan wasan na Sweden shi ne ya fara daga ragar Southampton ana shiga fili da minti 19, kafin Lingard ya kara ta biyu a minti na 38.

Manolo Gabbiadini ya rama wa Southampton kwallo daya dab da tafiya hutun rabin lokacine.

Bayan an dawo ne kuma minti uku da shiga fili, a minti na 48 kenan sai dan wasan (Gabbiadini )ya farke ta biyu.

Nasarar ta sa Manchester United ta rama abin da Southampton din ta yi mata na doke ta a wasan karshe na cin Kofin kalubale na FA a 1976.

Yanzu Zlatan Ibrahimovic ya ci wa Manchester United kwallo 26, da suka hada da biyun da ya ci Southampton, a wasan karshen na cin Kofin lig (EFL) a

Wannan shi ne kofi na 19 da ya dauka, kuma na farko da ya dauka a United.

Ya sheda wa tashar Sky Sports cewa: "Abin da ya kawo ni kenan, na zo na yi nasara ne''.

Ya ce, ''kana kara girma kana kara jin dadin nasara. Duk inda na je nasara nake yi. Ina ganin wannan shi ne kofi na 32 a wurina.''

Nasarar ta ba wa Jose Mourinho damar daukar babban kofinsa na farko a shekararsa ta farko a Mancester United.