Holland: Feyenoord ta kama hanyar daukar kofi

Haduwar Feyenoord da PSV
Bayanan hoto,

Maki 11 ne tsakanin Feyenoord da PSV ta uku a tebur

Feyenoord ta kara damarta ta cin kofin gasar lig din Holland, bayan da ta doke masu rike da kofin, PSV Eindhoven 2-1, wanda rabonta da dauka tun 1999.

Jens Toornstra ne ya fara ci wa Feyenoord din mai masaukin baki, minti tara da fara taka leda.

Sai dai kuma bakin sun farke kwallon ta hannun Gaston Pereiro a minti na 62.

An kusa tashi daga wasan ne, a minti na 84 sai Jan-Arie van der Heijden ya jefa kwallo ta biyo a ragar bakin da ka.

Sai dai an yi tababar shigarta raga, sai da aka yi amfani da bidiyon fasahar tantance shigar kwallo raga, aka tabbatar ta ci.

Yanzu maki biyar ne tsakanin Feyenoord da mai bi mata baya Ajax, bayan wannan nasara da ta yi ta goma a jere.