Kofin Afirka: Zambia ta doke Guinea 1-0

Zambia's Patson Daka
Bayanan hoto,

Patson Daka kenan, wanda ya ci wa Zambia kwallonta

Mai masaukin baki a gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka na 'yan kasa da shekara 20, Zambia ta fara sa'a a gasar inda ta ci Guinea 1-0 a Lusaka.

Patson Daka wanda ke wasa a kungiyar FC Liefering ta Austria shi ne ya ci kwallon da ta ba su nasara a minti na 48.

Guinea ta kusa farke kwallon a minti na 52 a wani hari da Momo Yassane ya kai da ka, amma mai tsaron ragar Zambian ya kare.

A ranar Laraba ne Zambia za ta yi wasanta na biyu da Mali.

Masar da Mali sun yi canjaras 0-0 a wasansu na rukunin na daya (Group A) a wasan na ranar Lahadi, wanda hakan ke nufin Zambia ce ke kan gaba a rukunin.

A ranar Litinin ne, a rukuni na biyu (Group B), Senegal za ta hadu da Sudan, yayin da Kamaru za ta kara da Afirka ta Kudu.

Dukkanin kasashe hudun da suka yi nasarar zuwa matakin wasan kusa da karshe, sun cancanci zuwa gasar cin Kofin Duniya ta matasa da za a yi a Koriya ta Kudu a watan Mayu.