Boksin: Pacquiao da Amir Khan za su dambata a Afrilu

Manny Pacquiao( a hagu) da Amir Khan (a dama) Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption In 2015, Khan ya ce an tsara zai kara da Pacquiao amma Manny din ba ya son haduwa da shi

Zakaran damben boksin na duniya na ajin matsakaita nauyi Manny Pacquiao zai kara da Amir Khan na Birtaniya ranar 23 ga watan Afrilu.

An hada damben ne bayan da Manny Pacquiao ya bukaci mabiyansa na shafin Twitter da su zaba masa abokin karawarsa na gaba, inda suka zabi Amir Khan.

An ruwaito Pacquiao mai shekara 38 dan kasar Philippines, ta shafukan sada zumunta yana cewa wannan shi ne abin da jama'a suke so.

Shi ma Amir Khan mai shekara 30 ya tabbatar da hada damben.

Sai dai ba a bayyana inda za a yi damben ba, ko da yake a baya Pacquiao, ya ce zai yi dambensa na gaba ne a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Khan ya bayyana a wani hoton bidiyo a shafukan sada zumunta na intanet yana cewa, ana duba yuwuwar yin damben a Birtaniya ko Dubai ko kuma Amurka.

A watan Mayu na 2016 ne Kahn ya yi dambensa na karshe lokacin da Saul 'canelo' Alvarez na Mexico ya yi masa dukan kwab daya.

Shi kuwa Pacquiao wanda zakaran aji-aji har shida ne na duniya, ya yi ritaya ne a watan Afrilu na shekarar da ta wuce, amma ya dawo ruwa, inda ya doke Jessie Vargas, a watan Nuwamba.