Real Madrid ta dawo kan tebur bayan ta doke Villareal 3-2

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Cristiano Ronaldo ya ci fanaretin da aka yi ce-ce-ku-ce a kanta

Real Madrid ta kado Barcelona daga kan teburin La Liga bayan da ta bi Villareal har gida ta doke ta 3-2.

Masu masaukin bakin ne suka fara cin Real Madrid 2-0 bayan hutun rabin lokacin inda Trigueros Muñoz ya ci ta farko a minti 50, sannan kuma Bakambu ya kara ta biyu a minti na 56.

Gareth Bale ne ya farke wa bakin ta farko a minti na 64, sannan kuma Ronaldo ya biyo baya da ta biyu da fanareti a minti na 74, kwallon da ta karya wa 'yan Villareal guiwa, har Morata ya zura musu ta uku a minti na 83.

Yanzu dai Real Madrid ta sake darewa matsayinta na daya, wanda Barca ta karba na dan kankanin lokacin a ranar Lahadin bayan da ita ma ta bi Atletico Madrid har gida ta doke ta 2-1.

Real Madrid yanzu tana da maki 55 da kuma kwantan wasa daya, yayin da Barcelona ke zaman ta biyu da maki 54.

Wasan Barcelona da Atletico Madrid

Bayan wasan, Barcelona ta hau kan teburin La Liga da maki 54 bayan da ta bi Atletico Madrid gida ta doke ta da ci 2-1, sai dai Real Madrid ka iya dawowa matsayin idan ta yi nasara a wasanta da Villareal.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Rafinha ne ya fara ci wa Barca kwallo a minti na 64, kafin Diego Godin ya farke, minti shida tsakani.

Sai dai an kusa tashi daga wasan ne a minti na 86 sai Lionel Messi ya ci kwallon da ta ba Zakarun na La Liga nasara.

Amma kuma Real Madrid, wadda take da kwantan wasa biyu ta koma kan teburin, bayan ta yi nasara a wasanta da Villarreal 3-2.

Yanzu Atletico, wadda ta dauki kofin na La Liga a shekarar 2014, tana matsayi na hudu da maki 45, tara kenan tsakaninta da ta daya.

Kwallon da Messi ya ci, ita ce ta 20 da ya jefa a wasa 21 da ya yi na La Liga a bana.

Haka kuma ita ce ta 21 da ya jefa ragar kungiyar Atletico Madrid a gasar La Liga.

Yanzu dai za a iya cewa fatan Atletico na daukar kofin bana na gasar ya kare, amma kuma wasa takwas ba tare da an ci ta ba, ciki har da nasara shida, abu ne da ya ba su kwarin guiwa.

Abin tambaya a nan yanzu shi ne ko Atletico za ta iya tsira da matsayin gurbin zuwa gasar kofin Zakarun Turai, yayin da ta biyar a tebur Real Sociedad ke bayanta da maki daya?

Ga sakamakon sauran wasannin La Liga da aka yi na ranar Lahadi 26 ga watan na Fabrairu

Espanyol 3 - 0 Osasuna

Athletic Club 3 - 1 Granada

Sporting Gijón 1 - 1 Celta de Vigo