An bannata motar 'yan wasan Crystal Palace

Motar safa ta 'yan wasan Crystal Palace

Asalin hoton, Jack Willis

Bayanan hoto,

Yadda aka zazzane motar 'yan wasan Crystal Palace

An lalata motar 'yan wasan Crystal Palace kafin wasanta na ranar Asabar da ta ci Middlesbrough 1-0, inda aka rubuta sunan kungiyar da kuma shafe ta da launin kungiyar.

Sabanin rade radin da ake yi, ba a ba wa 'yan wasan kungiyar Middlesbrough motar safar ba domin su yi amfani da ita, zuwa filin wasan.

'Yan wasan na Middlesbrough sun yi amfani da wata motar ne suka je wasan nasu na Premier.

Kakakin kungiyar ya bayyana cewa a ranar Juma'a da daddare ne aka zazzane motar tare da shafe ta da fenti, kafin wasan na ranar Asabar, wanda 'yan sanda sun tabbatar da hakan.