Lalata da 'yan wasa: Gradi zai daukaka kara

Dario Gradi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dario Gradi wanda tsohon kocin Chelsea ne, ya kuma horar da 'yan wasan kungiyar Crewe daga 1983 zuwa 2007

Darektan kwallon kafa na kungiyar Crewe, Dario Gradi zai daukaka kara kan dakatar da shi da hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta yi masa na shiga harkokin wasan.

An dakatar da Gradi mai shekara 75 ne ranar 25 ga watan Nuwamba, kafin hukumar ta yi bincike kan tarin zargin lalata da yara, a kungiyoyin kwallon kafa.

Ana ganin tuni lauyoyinsa sun tattara bayanai daga 'yan wasa da koci-koci da kuma manyan shugabannin kungiyoyin kwallon kafa da ya yi aiki da su a baya.

Sai dai abin da ba a sani ba shi ne, ko dakatarwar ta shafi zargin da aka yi ne cewa lokacin da yake kocin Chelsea a shekarun 1970, ya ziyarci gidan wani matashin dan wasa mai shekara 15, domin bayar da hakuri kan cin zarafin da aka yi wa matashin na lalata da shi, da babban mai nemo wa kungiyar 'yan wasa Eddie Heath ya yi, ko kuma dakatarwar kan abubuwan da suka faru ne lokacin yana darektan kwallo a kungiyar Crewe.

Mutane da yawa sun zargi Heath, wanda tuni ya mutu, da laifin lalata da su a shekarun 1970 da kuma 1980.

Gradi ya gaya wa abokansa cewa a shirye yake ya wanke sunansa, kuma ya ce matakin na FA, ya tayar masa da hankali, abin da yake gani ya sa aikinsa cikin hadari.