Zan yi shawara kan zamana a Man Untd— Ibrahimovic

Ibrahimovic da Mourinho

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Zlatan Ibrahimovic ya ce 'ya'yansa ne da Mourinho suka sa ya koma Manchester United

Zlatan Ibrahimovic ya ce zai duba ya yi nazari kan maganar tsawaita zamansa a Manchester United, amma kuma ya ce 'ya'yansa ne suka roke shi ya je kungiyar a shekarar da ta wuce.

Ibrahimovic, mai shekara 35, ya bar Paris St-Germain ne a watan Yuli, inda ya kulla yarjejeniyar shekara daya a Old Trafford, tare da zabin kara wata shekarar.

Kocin United Jose Mourinho ya yi amanna dan wasan na Sweden zai tsaya, amma kocin ya kara da cewa shi dai bai taba rokon wani dan wasa ya kulla kwantiragi a kungiyarsa ba.

Ibrahimovic ya ce muna da sauran wata biyu kafin kakar ta kare. Mu bari mu ga yadda abubuwa za su kasance.

Ya ce, wani ya kirkiri labarin cewa, wai idan ba su samu gurbin zuwa gasar cin kofin ZakarunTurai ba, ba zai ci gaba da zama a United ba. Ya ce wannan karya ce kawai.

Bayan da Ibrahimovic ya ci kwallon da ta sa United ta dauki Kofin Lig, a wasan da suka doke Southampton 3-2 a ranar Lahadi, Mourinho ya ce magoya bayan kungiyar za su iya zuwa gidan dan wasan su yi zaman dirshan , su roke shi ya tsaya.

Ibrahimovic ya ce kyakkyawar alakarsa da Mourinho wanda ya yi masa koci a Inter Milan, ita ce ta sa ya koma United, amma ba wannan ba ce kadai.

Ya ce ko alama zuciyarsa ba ta kungiyar, amma kuma sai 'ya'yansa suka rika rokonsa cewa suna son su ga yana wasa a United, a lokacin da yake shirin barin zakarun faransa PSG.

Ya ce ana cikin hakan ne sai Jose Mourinho ya yi masa waya, ya ce abin da ya tambayi kocin kawai shi ne ya gaya masa lambar da zai sa idan ya zo.

Dan wasan ya kara da cewa 'ya'yansa sun gamsu da abin da yake yi, amma kuma a yanzu shi ne shugaba ba su ba.