Shakespeare na son maye gurbin Ranieri a Leicester

Shakespeare da Ranieri kafin korar kocin dan Italiya

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Bayan korar Ranieri, Shakespeare ya samu mukamin kocin rikon kwarya daga mataimaki

kocin rikon kwarya na Leicester City Craig Shakespeare yana da kwarin gwiwar samun aikin kocin kungiyar na dindindin, bayan korar Claudio Ranieri.

Shakespeare wanda mataimakin Ranieri ne, yana da kyakkyawar alaka da jituwa da 'yan wasan kungiyar.

Craig mai shekara 53 zai iya rike kungiyar har zuwa akalla karshen kakar wasanni ta bana, idan har kungiyar ta tabuka wani abin kirki a wasanta da Liverpool a ranar Litinin.

Kungiyar ta Leicester dai ita ce ta dauki kofin Premier a bara, amma yanzu za ta yi wasanta da Liverpool din ne tana cikin rukunin masu faduwa daga gasar.

Babu takamaiman lokacin da ake sa ran za a bayyana sabon kocin,sai dai idan Shakespeare yayi nasara a wasansu na gida da Hull City ranar Asabar, wasan da ke da muhimmanci ga dukkanin kungiyoyin biyu, nasarar da za ta ba shi damar samo maki hudu daga cikin shida, sannan kuma idan sun yi kokari, to hakan zai iya ba shi damar samun mukamin.