Alex Young: Tsohon dan wasan Hearts da Everton da Scotland ya mutu

Alex Young yayin da Everton ta dauki kofin FA a 1966

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Alex Young (a dama) dauke da kofin FA da Everton ta ci a 1966

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar Hearts da Everton da kuma tawagar yankin Scotland Alex Young ya mutu yana da shekara 80.

Young ya yi wasa a Hearts daga 1955 zuwa 1960 kuma kwallayen da ya ci a lokacinsa sun taimaka wa kungiyar ta Edinburgh ta ci kofin gasar Scotland a 1958.

Dan wasan ya samu shiga kungiyar Everton, inda ya buga mata wasa 273, kuma ya ci mata kwallo 87, abin da ya kai su ga daukar kofin rukuni na daya da kuma kofin FA.

Haka kuma Young ya yi wa kasarsa wasa sau takwas, inda ya ci kwallo sau biyar.

'Yan kallo sama da 20,000 suka halarci wasan karrama shi da Everton ta yi a shekara ta 2001 a filinta na Goodison Park.