Andries Jonker ya bar Arsenal ya koma Wolfsburg

Andries Jonker

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Andries Jonker ya yi aiki karkashin Louis van Gaal a Barcelona da Bayern Munich

Andries Jonker: Wolfsburg ta dauki kocin kungiyar matasan 'yan wasan Arsenal, a matsayin kocinta na uku a bana, bayan da kungiyar ta kori Valerien Ismael.

Jonker, mai shekara 54, ya koma Wolfsburg din ne bayan da ya bar ta shekara uku da ta wuce a matsayin mataimakin koci, ya je ya kama aiki da Arsenal.

Kocin dan kasar Holland ya kama aikin ne na yanzu, yayin da kungiyar ta Jamus ke da maki biyu tsakaninta da rukunin faduwa daga gasar Bundesliga.

Jonker ya ce abin da yake da muhimmanci a yanzu shi ne su hanzarta samun maki 40 domin tsira a gasar.

A ranar Lahadi ne kungiyar ta kori Ismael, kwana biyu da Werder Bremen ta bi su gida ta doke su 2-1.

Wannan shi ne karo na hudu da aka ci su a wasa biyar na gasar, abin da ya sa suke da maki 22, yayin da ya rage wasa 12 a kammala gasar ta bana, inda suke matsayi na 14 a teburin mai kungiyoyi 18.

Wasan farko da Jonker zai jagoranci kungiyar shi ne wanda za ta hadu da Mainz wadda ke matsayi na 11, ranar Asabar ( karfe 3:30 na yamma agogon Najeriya).