Tennis: Roger Federer ya yi nasara a gasar Dubai

Roger Federer Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wannan shi ne karo na 13 da Roger Federer ke halartar gasar Dubai

Roger Federer ya ci wasansa na farko inda ya fitar da dan Faransa Benoit Paire a gasar Dubai, tun bayan da ya ci babban kofinsa na 18 a gasar Australian Open.

Dan wasan na Switzerland mai shekara 35, wanda shi ne gwani na 10 a duniya, ya fitar da abokin karawar tasa ne cikin minti 54 kawai, da ci 6-1 6-3, inda yanzu zai hadu da Mikhail Youzhny ko Evgeny Donskoy.

Federer wanda shi ne na uku a duniya bai halarci gasar ta Dubai ba ta bara sakamakon ciwon guiwa.

Harwayau a gasar, Andy Murray ya sha kashi a hannun dan uwansa dan Birtaniya Dan Evans a zagayen farko na wasan maza na bibbiyu.

Evans da Gilles Muller ne suka doke Murray da Nenad Zimonjic da ci 6-1 7-6 (7-2) .

Murray wanda shi ne na daya a duniya zai dawo wasan 'yan dai-dai ranar Talata, inda zai fafata da Malek Jaziri, na Tunisiya, wanda yake matsayin na 51 a duniya.