Fatara ta sa hatsabibiyar 'yar wasan Soviet sayar da lambobinta na yabo

Olga Korbut a gasar Olympics ta Munich

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Olga Korbut ta ci lambobin zinare uku da azurfa daya a gasar Olympics ta Munich ta 1972

Olga Korbut 'yar wasan wuntsule-wuntsule ta Soviet (tsohuwar Rasha), wadda ta burge duniya a gasar Olympics ta Munich a 1972, ta sayar da tarin lambobi da kofunan da ta ci a wata kasuwar sayar da kayan tarihi a Amurka.

A abubuwan da ta sayar guda bakwai, wadanda suka hada da lambobin zinare biyu da na azurfa da ta ci a gasar Olympics din ta Munich, ta samu dala 183,300, kwatankwacin sama da naira miliyan 100.

Korbut, wadda aka haifa a Belarus, ta yi kaura zuwa Amurka a 1991, yanzu tana zaune ne a Arizona.

A wani rahoto da kafar watsa labarai ta intanet ta Gazeta.ru ta Rasha ta yi ta ce tsohuwar 'yar wasan hatsabibancin tana cikin matsalar kudi, inda kafar ta yi wa labarin taken: ''Lambobin yabo sun ceto Korbut daga yunwa.''

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Korbut mai shekara 61, yanzu tana zauna ne salun-alun a Arizona

A shekarar 1972, lokacin tashen yakin cacar-baka (tsakanin Rasha da Amurka), hatsabibancin da Korbut ta yi a wasan wutsuttsule ya jawo mata farin jini a kasashen Yammacin duniya, lokacin tana 'yar shekara 17.

Haka kuma murmushi da faran-faran da take yi da kuma kyawunta sun sa ta yi suna ta zama abar tarihi a fagen wasannin Olympic.

Asalin hoton, SCREENSHOT - HERITAGE AUCTIONS

Bayanan hoto,

Daya daga cikin lambobin zinaren da Korbut ta ci a gasar 1972

A shekarar 1976 ta sake cin lambar zinare da ta azurfa a gasar wasanni ta Montreal, a kasar Canada.

Daga cikin wuntsulen hatsabibancin da ta yi a lokacinta, wanda aka yi masa lakabin sunanta, Korbut Flip, a yanzu an hana yinsa a gasar Olympics saboda yana da hadari sosai.

Daga shekarar 1978 zuwa 2000 Korbut ta auri Leonid Bortkevich, sanannen mawakin nan na lokacin tsohuwar Tarayyar Soviet, wanda suka yi kaura tare zuwa Amura bayan rushewar Tarayyar Soviet din a 1991.

Olga Korbut Tana da da ake kira Richard.