Valcke ya daukaka kara kan hukuncin Fifa

Jerome Valcke

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A shekara ta 2007 ne Jerome Valcke ya zama babban sakataren Fifa

Tsohon na hannun daman, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Sepp Blatter, ya daukaka kara kan hukuncin hana shi shiga harkokin kwallon kafa na shekara 10 da aka yi.

A shekarar da ta wuce ne aka yi wa Jerome Valcke, wanda a da shi ne babban sakataren Fifa, saboda samunsa da laifin cuwa-cuwa a harkar sayar da tikitin kallon gasar cin Kofin Duniya

A yanzu dan Faransan mai shekara 56, ya daukaka kara ne, inda yake bukatar kotun sauraren kararrakin harkokin wasanni ta duniya ta rushe wannan hukunci da aka yi masa, yana mai nanata cewa ba abin da ya yi da ya saba ka'ida.

Da farko dai Fifa ta yi masa haramcin shekara 12 ne tare da cin tararsa fan 70,800, kusan naira milina 50, amma daga baya ta rage tsawon haramcin zuwa shekara 10.

Bayan samunsa da laifi a cuwa-cuwar sayar da tikitin kallon, kwamitin da'a na Fifa ya ce tsohon sakatare janar din nata ya yi abubuwan da suka saba wa hukumar, wadanda suka jawo mata asarar dimbin kudade.

Daga cikin abubuwan da kwamitin ya ce, ya yi har da daukar hayar jirage ya tafi yawon shakatawa da iyalansa, da kudin Fifa.

Sannan kwamitin ya zarge shi da sayar da damar nuna wasanni a talabijin, a kan kasa da farashin da ya kamata, kuma an zarge shi da kokarin kawo tarnaki a binciken da ake yi masa, ta hanyar kokarin goge wasu bayanai da suka shafi binciken.

A watan Disamba, kotun sauraren kararrakin harkokin wasannin ta duniya ta yi watsi da bukatar tsohon shugaban Fifa, Sepp Blatter, ta neman a soke haramcin shiga harkokin wasanni na shekara 6 da aka yi masa, kan saba ka'idojin hukumar.