Badala: Tsohon dan wasan Ingila Adam Johnson ya nemi daukaka kara

Adam Johnson

Asalin hoton, PA/DURHAM POLICE

Bayanan hoto,

An daure tsohon dan wasan na Sunderland shekara shida

Tsohon dan wasan Ingila Adam Johnson, wanda aka yi wa hukuncin daurin shekara shida kan kulla alakar lalata da wata yarinya 'yar shekara 15, zai sake zaman tsammanin samun damar daukaka kara.

A watan Maris na shekarar da ta wuce ne aka samu Johnson mai shekara 28 da laifin tabawa da kuma kulla alakar soyayya da wata yarinya, 'yar makaranta mai shekara 15.

Bayan hukuncin ya nemi ya daukaka kara, aka hana shi wannan dama, amma kuma a kusan karshen shekarar da ta gabata ya sake gabatar da bukatar a karo na biyu.

Wani kwamitin alkalai guda uku ne zai yi nazari kan sabuwar bukatar tasa a kotun daukaka kara ta Ingila, inda a nan gaba za a yanke hukunci kan maganar.

A baya tsohon dan wasan na Sunderland ya amince da laifin da aka tuhume shi da shi, na kulla alakar soyayya da yarinyar, da kuma wata tuhumar ta badala da ita.