Kofin Jamus: Makasan maza za su hadu da Dortmund

'Yan wasan Sportfreunde Lotte

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

'Yan wasan na Sportfreunde Lotte na rukuni na uku sun yi waje da manyan kungiyoyi uku na Jamus daga gasar

Makasan maza, 'yan kungiyar Sportfreunde Lotte, da ke rukuni na uku, za ta kara da Borussia Dortmund a wasan dab da na kusa da karshe na cin kofin kalubale na Jamus.

Tuni daman kungiyar ta yi waje da manya-manyan kungiyoyi irin su 1860 Munich da Werder Bremen da Bayer Leverkusen daga gasar ta cin kofin na Jamus.

An kiyasta darajar gaba daya 'yan wasansu a kan euro miliyan hudu da rabi, yayin da ta abokan karawarsu Dortmund ta kai euro miliyan 740.

Sannan 'yan kallo 10, 059 filinsu yake dauka, yayin da na Borussia Dortmund (Westfalenstadion) yake cin mutane 81,360.

Kociyansu Ismail Atalan ya ce, wasan na Talata ba abu ne mai sauki ba, amma duk da haka ko Aubameyang ba zai je ko'ina ba, za a taka masa birki.

Haka su ma magoya bayansu, ba sa wata fargaba, kamar yadda wani mai suna Rainer Lammers ya ce:

Ina ganin kyakkyawar dama, domin tuni mun yi waje da kungiyoyi uku daga gasar, yanzu kuma ga wata babbar giwar a gabanmu.