Mbokani ya tafi jinyar sati shida

Dieumerci Mbokani Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A wasa 12 da Dieumerci Mbokani ya yi wa Hull har yanzu bai ci kwallo ba

Dan wasan gaba na Hull Dieumerci Mbokani ba zai sake wasa ba nan da mako shida saboda jinyar da zai yi ta ciwon da ya ji a cinyarsa.

An yi canjin dan wasan ne na DR Congo mai shekara 31, wanda yake zaman aro na shekara daya daga kungiyar Dynamo Kiev, a wasan da suka yi 1-1 ranar Asabar da Burnley.

Haka kuma kungiyar ta Hull ta tabbatar da cewa raunin da dan bayanta Harry Maguire ya ji a guiwa a wasan na Burnley, bai yi tsananin da aka yi tsammani ba.

Hakan na nufin watakila dan wasan mai shekara 23 ya yi wasan da Hull din za ta ziyarci masu rike da kofin na Premier Leicester City, ranar Asabar.