Chisom Egbuchulam ya samu kungiya a Sweden

Chisom Egbuchulam na sanya hannu a kwantiragi da BK Hacken Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Chisom Egbuchulam yayin da yake sanya hannu a kwantiraginsa da BK Hacken

Dan wasan gaba na Najeriya Chisom Egbuchulam ya tafi kungiyar BK Hacken ta Sweden a matsayin aro na shekara shekara daya daga Enugu Rangers.

A bisa yarjejeniyar tafiyar tasa, yana da damar zama a kungiyar, wadda ta dauki kofin kalubale na Sweden na 2016, na dindindin tsawon shekara uku.

Dan wasan mai shekara 25 a kakar da ta wuce ya ci wa Rangers kwallo 16, kuma ya bayar aka ci 11, abin da ya taimaka wa kungiyar ta dauki kofin Premier na Najeriyar, sanna ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin Zakarun Afirka.

A hirasa da BBC Egbuchulam ya ce tafiyar tasa Turai, wani babban mafarki ne da yake yi wanda ya tabbata.

Kuma ya godewa Allah da kuma kungiyar ta BK Hacken kan damar ta yin wasa a Turai.

Kokarin dan wasan a gasar lig ta Najeriya, ya sa kocin tawagar kasar Gernot Rohr ya gayyace shi domin ya buga wasan neman gurbin gasar cin Kofin Duniya na 2018 da Zambia a watan Oktoba.