Leicester na tattaunawa da Roy Hodgson

Roy Hodson Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Hodgson ya kuma jagoranci City da Blackburn a Ingila a aikinsa na kociya

Zakarun gasar Firimiya, Leicester City sun tattauna da tsohon kociyan Ingila, Roy Hodgson, domina ya zama kociyansu.

Amma ana zaton kocin mai shekara 69 daya ne kawai daga cikin wadanda aka tattauna da su wajen neman wanda zai maye gurbin Claudio Ranieri.

Kuma kociyan kungiyar na wucen-gadi, Craig Shakespeare, zai iya ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa karshen kakar bana idan kulab din ya ci gaba da samun nasara.

An sallami Ranieri ne ranar 23 ga watan Fabrairu, wata tara bayan ya lashe gasar.