Dan Nigeria ya rubuta jarrabawa a filin jirgin saman Amurka

Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan Najeriyan ya je Amurka ne domin aikin fasaharar manhajar da ke da alaka da intanet

An tilastawa wani dan Najeriya rubuta jarabawar tabbatar da cewar ya kware a aikinsa bayan ya sauka a filin jirgin sama na JFK da ke New York.

Injiniyan manhajar da ya fito daga jihar Legas yana ikirarin cewar an saka shi rubuta jarabawar ne domin jami'ain ba su yarda da ikirarin da ya yi na abubuwan da ya iya ba.

Shafin sadarwa na Linkedin ya ce , Celestine Omin, dan shekara 28, ya sauka a filin jirgin John Kennedy ranar Lahadin da ta gabata bayanya shafe sa'oi 24 a jirgi daga Najeriya.

Mista Omin ma'aikacin wani kamfanin samar da masu gina manhaja ne da ake kira Andela wanda ya ke da ofisoshi a New York da Lagos da Nairobi da kuma San Francisco.

Kamfanin ya ce Mista Omin yana hayan masu gina manhajan da suka fi kwarewa a nahiyar Afirka, kuma yana hada su da masu neman gurbin aiki.

A bara ne dai Shugaban Facebook, Mark Zukerberg ya ziyarci ofishin Andela a Lagos.

Rahotanni sun ce an bai wa Mista Omi izinin shiga kasar na wucin gadi domin ya yi aiki da kamfanin fasahar kasuwanci na First Access da ke gundumar Manhattan a New York.

'Gaskiya ko karya?'

Bayan jami'ai sun mishi wasu tambayoyi, sai aka shigar da shi wani daki domin ci gaba da bincike.

Rahotanni sun ce wani jami'i ya tambayi Mista Omi cewar: "Takardar bisar ka ta ce kai injiniyan manhaja ne. Gaskiya ne?"

Sannan aka ba shi takarda da alkalami kuma aka gaya masa ya amsa tambayoyi biyu domin tabbatar da cewar injiyan manhaja ne.

Mista Omin ya shaida wa LinkedIn cewar da alamu ba kwararre bane ne ya samo tambayoyin da aka yi masa da shafin binciken Google.

Daga baya bayyana a shafin Tiwtter cewar ya yi irn gajiyar da ta hana shi tunani kuma ya shaida wa jami'in cewar za su iya tattaunawa kan wasu fannonin kimiyyar kofuta.

Bayan ya bayar da amsoshin tambayoyin, jami'in ya shaida masa cewar ya fadi jarawaban.

Ya ce shi ya zaci ana so ya yi bayanani ne kan shafin wikipedia na intanet.