Moses zai zauna a Chelsea har 2021

Victor Moses a lokacin da yake murnar zura kwallo a ragar Tottenham a watan Nuwamba Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Kwallon da Victor Moses ya ci ta baya-bayan nan ita ce ta wasan da suka doke Tottenham 2-1 a watan Nuwamba

Dan wasan baya na gefe na Chelsea Victor Moses ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar da karin shekara biyu, inda zai ci gaba da zama a Stamford Bridge har shekara ta 2021.

Moses, mai shekara 26, wanda ya yi kakar wasa uku a baya a zaman aro a Liverpool da Stoke City da West Ham, a yanzu ya zama daya daga cikin 'yan wasan kungiyar na kullum karkashin jagorancin kocinsu Antonio Conte.

Dan wasan na Najeriya wanda ya ce ya ji dadin hakan, ya kara da cewa, yana jin dadin wasansa a karkashin Conte, wanda ya ce yana karfafa wa kowane dan wasa guiwa.

Moses, wanda Chelsea ta sayo daga Wigan akan fan miliyan 9 a watan Agusta na 2012, ya yi wa kungiyar wasa 28, inda ya ci mata kwallo 4 a bana.

Tun lokacin da aka dawo da shi wasa a gefen dama na baya, a tsarin 3-4-3 , inda suka bi Hull City suka doke ta da ci 2-0 a ranar 1 ga watan Oktoba, ake fara sa shi a dukkanin wasan da Chelsea za ta yi.

Tun daga wannan nasara da ta yi, Chelsean ta ci wasanninta 16 daga cikin 19 na gasar Premier, inda suka bayar da ratar maki goma a matsayi na daya.