West Brom ta samu dan bayan da ya fi 'yan gabanta cin kwallo

Gareth McAuley (a tsakiya) lokacin da yake jefa kwallo ragar Bournemouth Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Gareth McAuley (a tsakiya) lokacin da yake ci wa West Bromwich kwallon da ta doke Bournemouth

Abu ne mai wahala a wasan kwallon kafa a ce ga dan bayan da ya zama wanda ya fi kowa cin kwallo a kungiyarsa.

Musamman ma a ce dan wasan ya kai shekara 37 kamar Gareth McAuley, na kungiyar West Bromwich Albion.

Dan wasan na Ireland ta Arewa, wanda bai fara buga wasan kwallon kafa na kwararru ba sai da ya kai shekara 24, ba irin mutanen da za su yi tunkaho da bugun kirji ba ne kan irin wannan bajinta, ta zama wanda ya fi ci wa kungiyar tasa kwallo, a bana, tare da Salomon Rondon dan Venezuela.

McAuley tare da Rondon, sun ci wa kungiyar tasu kwallo bakwai-bakwai ne a kakar wasa ta bana.

Sai dai 'yan wasa daban-daban ne har 11 suka ci wa kungiyar kwallonta 36 a wasanninta 26 na Premier a bana.

Haka kuma shi dai McAuley ya kan ci kwallonsa ne kusan a lokaci na musamman, da ake matukar bukata, a kungiyarsa da kuma tawagar kasarsa.

Tun bara lokacin da ya ci wa Albion kwallo daya kawai, a bana sau tara yana jefa kwallo a raga, da suka hada da biyu da ya ci wa Irealand ta Arewa.

Hakkin mallakar hoto others
Image caption Gareth McAuley ya ci wa Ireland ta Arewa kwallo tara, daidai da yadda George Best ya ci mata

Bayan kwallon da ya ci a gasar Kofin kasashen Turai a wasansu da Ukraine, da kuma wadda ya ci kansu lokacin da Wales ta fitar da su, McAuley ya ci Azerbaijan a wasansu na neman gurbin gasar Kofin Duniya.