Celtic ta bai wa Hibs Efe Ambrose na Najeriya aro

Brendan Rodgers ba ya amfani da dan wasan na Najeriya Hakkin mallakar hoto SNS
Image caption Wasa biyu kawai na wata gasa Efe Ambrose ya yi tun da Brendan Rogers ya zama kocin kungiyar

Kungiyar Hibernian ta Scotland, wadda ke fama da matsalar jinyar 'yan wasa ta karbi aron babban dan bayan Celtic, Efe Ambrose, har zuwa karshen kakar bana.

Dan wasan na Najeriya mai shekara 28, wanda daman kocin kungiyar ta Hibs ne Neil Lennon ya kai shi Celtic, rabonsa da ya yi mata wasa tun watan Yuli.

Yunkurin tura dan wasan aro kungiyar Blackburn Rovers, ya ci tura a ranar Litinin, saboda matsalar samun takardar izinin aiki ga dan wasan.

Haka kuma kungiyar ta Hibs ta dauki aron tsohon dan wasan baya na kungiyar Motherwell da Falkirk da Dundee United da kuma Ross County Brian McLean, mai shekara 32, sakamakon jinyar da manyan 'yan wasanta na baya uku suka tafi.

Paul Hanlon da Liam Fontaine da kuma Jordon Forster dukkaninsu na fama da rauni, yayin da dan wasansu daya na baya da yake da lafiya, Darren McGregor, shi kuma an dakatar da shi.

Dan wasan ba zai yi wasansu na ranar Asabar na matakin dab da na kusa da karshe na kofin kalubale na Scotland ba wanda kungiyar za ta yi da Ayr United.