Kwayoyi: Phelps ya ce bai taba yin gasar da ba marassa laifi a cikinta ba

Phelps na murnar cin lambar zinare Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Phelps ya ci biyar daga cikin lambobinsa na zinare na Olympic 23 a gasar Rio ta 2016

Dan wasan da ya fi cin lambobin bajinta na gasar Olympic a tarihi Michael Phelps, ya ce ya yi amanna bai taba yin gasar duniya da 'yan wasan da gaba daya za a ce ba mai amfani da abubuwan kara kuzari a cikinsu ba.

Shi dai tsohon zakaran wasan iyon dan Amurka mai shekara 31, yana son 'yan majalisar dokokin Amurka ne su matsa domin aiwatar da sauye-sauye a dokokin duniya na hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni.

Phelps din ya yi kalamin ne a lokacin da yake bayar da sheda a zaman majalisar wakilan Amurka kan yadda za a inganta matakan yaki da ta'adar amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni.

Gwamnatin Amurka tana taimaka wa da kudi wajen tafiyar da ayyukan hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta duniya (wada), kuma kwamitin majalisar wakilan Amurkan zai iya bayar da shawarar kara wa hukumar kudi.

Phelps, wanda ya ci lambobin zinare 23 na gasar Olympic ya kara da cewa, a gaba dayan lokacin da yake wasa, yana tunanin wasu 'yan wasan suna amfani da abubuwan kara kuzari, kuma ta tabbata an kama wasu daga cikinsu da yake zargi.