Barcelona ta hau teburin La Liga bayan ta ci Sporting Gijon 6-1

Lionel Messi lokacin da ya ci kwallon farko Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lionel Messi ne ya fara ci wa Barcelona kwallo da ka, wadda ita ce da ya ci ta 36 a wasa 36 da ya yi a bana

Barcelona ta sake darewa kan teburin La Liga bayan da ta yi kaca-kaca da Sporting Gijon da ci 6-1 a Camp Nou.

Lionel Messi ne ya fara daga ragar bakin da ka a minti na tara, sannan Rodriguez ya ci kansu minti biyu tsakani.

Sporting ta samu damar rama kwallo daya lokacin da aka kai minti 21 da wasa, amma kuma bayan minti shida sai Suarez ya ci ta uku.

Paco Alcacer ya kara wa Barcelona kwallonta ta hudu a minti na 49, kafin kuma Neymar shi ma ya biy baya da tasa, wadda ita ce ta biyar a minti na 65.

Can kuma wasa ya kusa karewa a minti na 87 sai Rakitic ya ci cikammakin kwallon ta Barcelona ta shida kenan.

Da wannan nasara yanzu Barcelonan ta zama ta daya a tebur da maki 57 akalla kafin a san yadda wasan Real Madrid mai maki 56, da kwantan wasa daya, zai kaya da Las Palmas, nan da dan lokaci, a Larabar.

Sai dai kuma dubban magoya bayan Zakarun na La Liga sun ki zuwa kallon wasan saboda haushin yadda Barcelonan ta sha kashi 4-0 a hannun PSG a gasar Kofin Zakarun Turai, a watan Fabrairu da ya kare.

A daya daga cikin wasannin na Larabar nan Villareal ta je gidan Osasuna ta lallasa ta da ci 4-1. Sakamakon ya sa Villareal ta zama ta 6 da maki 42, yayin da Osasuna take ta karshen tebur (20) da maki 10.