Ban san matsayina ba a Manchester City

Sergio Aguero lokacin da ya ci Huddersfield Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sergio Aguero ne na uku a jerin wadanda suka fi ci wa Man City kwallo a tarihi

Dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero ya ce har yanzu kungiyar ba ta yi masa magana ba a kan ko zai ci gaba da zama ko ko kuma za ta sake shi a karshen kakar nan ba.

Ana dai ta rade radi ne a kan makomar dan wasan, tun a watan da ya gabata, bayan da dan wasan Brazil Gabriel Jesus mai shekara 19 ya maye gurbinsa a kungiyar.

Kocinsu Pep Guardiola ya ce yan son rike Aguero mai shekara 28,wanda kwantiraginsa da kungiyar har zuwa 2020 ne, amma dan wasan yanzu ya ce bai yi wata tattaunawa kan zamansa a City din ba.

Aguero ya ci kwallo hudu a wasansa biyu, bayan da ya sake samun gurbinsa, saboda jinyar raunin da Jesus yake yi, wadda ta sa kila ba zai kara wasa ba har karshen kakar nan.

Sau biyu ya zura kwallo a raga, a maimaicin wasan zagaye na biyar na kofin FA, wanda suka ci Huddersfield 5-1 ranar Laraba, wanda hakan ya sa a yanzu kwallon ya ci ta kai 22 a bana.

Kocin nasu Guardiola ya bayyana cewa wannan shi ne wasa mafi kyau da Aguero ya yi a kakar nan.

Aguero shi ne na uku a jerin 'yan wasan da suka fi ci wa City kwallo a tarihi, inda yake da 158, 20 tsakaninsa da Eric Brook, wanda shi ne na daya, sanna kuma takwas tsakaninsa da na biyu Tommy Johnson.

Dan wasan Argentinar na gaba ya ce ba ya kaunar barin City, wadda ya koma daga Atletico Madrid a kan fan miliyan 38 a 2011, amma yanzu za a saurara zuwa karshen kakar nan kafin a san makomarsa a kungiyar.

Aguero ya ce, a ko da yaushe yana cewa za a ga abin da zai kasance a watan Yuni, kungiyar za ta iya fadr komai da take so, amma dole ne a wannan watan na Yuni su gana da shi.

Ya kara da cewa niyyata, ita ce na tsaya to amma lokaci ne mai tsawo. Ina da watanni uku da zan yi kokarina, kuma kila idan mun yi sa'a mu ci wani kofi.