Kocin Barcelona Luis Enrique zai bar aiki a karshen kaka

Kocin Barcelona Luis Enrique Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Luis Enrique na cikin shekara ta uku kuma ta karshe a Barcelona

Kocin Barcelona Luis Enrique zai bar kungiyar a karshen kakar wasan da ake ciki, bayan shekara uku da ya yi a kulob din domin ya samu ya huta kamar yadda ya ce.

Kocin mai shekara 46, ya bayyana hakan ne bayan wasansu na La Liga na ranar Laraba da suka casa Sporting Gijon 6-1.

A shekararsa ta farko ya dauki Kofin Zakarun Turai daga cikin manyan kofuna uku da ya ci a lokacin, sannan kuma a kakar da ta gabata ya jagorance suka dauki manyan kofuna biyu na kasar.

Sai dai kuma a yanzu suna kan gabar ficewa daga gasar Kofin Zakarun Turai, bayan da Paris St-Germain ta doke su 4-0 a wasansu na farko na zagayen kungiyoyi 16.

Enrique ya ce, maganar barin aikin nasa, shawara ce mai wuya, amm kuma wadda ya tsaya ya yi tunani sosai a kanta, wadda kuma ya ga ya dace ya bi shawarar, ya bar aikin a karshen kwantiraginsa a wannan bazara.

Kocin ya kara da cewa ya yanke wannan shawara ne ba don komai ba, sai dai kawai domin ya samu ya huta.

Ya ce, abu mafi muhimmanci shi ne, muna da sauran wata uku masu ban sha'awa suka rage mana a gasa uku da ke gabanmu, wadda a daya daga cikinsu, muna cikin tsaka-mai-wuya, amma idan muka yi sa'a za mu iya tsira.

Nasarar da Barca ta yi a kan Sporting ta sa ta zama ta daya a teburin La Liga, da maki daya tsakaninta da Real Madrid, wadda take da kwantan wasa daya.

Yanzu dai zakarun na La Liga za su hadu da Alaves a wasan karshe na gasar kofin Copa del Rey (King's Cup), ranar 27 ga watan Mayu.

Enrique wanda tsohon dan wasan tsakiya ne na Spaniya, ya yi wasa a Barcelona tsakanin 1996 har ya yi ritaya daga wasa a 2004.

Daga nan ne kuma ya yi aikin horar da matasan kungiyar ta Barcelona daga 2008 zuwa 2011, sannan kuma ya zama kocin babbar kungiyar, bayan ya je ya yi aikin horar da Roma da Celta Vigo.