Tsohon dan wasan Celtic da Scotland Gemmel ya mutu

Tommy Gemmell Hakkin mallakar hoto SNS
Image caption Gemmell ya mutu ne bayan ya dade yana jinya

Kungiyar Celtic ta yi jimamin mutuwar tsohon dan wasanta na baya da kungiyar Lisbon Lion da kuma Scotland, Tommy Gemmell, wanda ya mutu yana da shekara sakamakon doguwar jinya da ya yi.

Tsohon dan wasan bayan na Scotland ya ci kwallo a lokacin da suka doke Inter Milan 2-1 a 1967, lokacin da Celtic ta zama kungiyar farko ta Birtaniya da ta dauki Kofin Zakarun turai.

Haka kuma Gemmell din ya zura kwallo a raga a wasan karshe na Kofin Zakarun Turai na shekarar 1970, wanda Celtic ta yi rashin nasara a hannun Feyenoord da ci 2-1.

Marigayin ya yi shekara 10 a Celtic, tsakanin 1961 da 1971, inda ya yi mata wasa 418, kuma ya ci kwallo 63.

Haka kuma Gemmell ya yi wa Scotland wasa 18, inda ya fara taka wa yankin leda a wasansu da Ingila a watan Afrilun 1966.

Shugaban kungiyar ta Celtic Peter Lawwell ya bayyana ta'aziyyarsu da kuma jimamin mutuwar Gemmell, wanda ya bayyana a matsayin ''babbar giwar Celtic ta gaskiya".