Labarin gurgun dan wasan Mancester City

Jamie Tregaskiss a lokacin atisaye Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Manchester City ta gano Jamie Tregaskiss ne tun yana shekara 10

Jamie Tregaskiss ya rasa kafarsa ne sakamakon cutar daji ta kashi da ta kama kafarsa ta hagu tun lokacin yana dan shekara 13, amma kuma yanzu ya ci gaba da taka leda a kungiyarsa ta Manchester City.

A lokacin ya yanke kauna ba zai sake taka leda ba, amma yanzu yana yi wa kungiyar Manchester City ta guragu wasa.

Bayan an yanke masa kafar da dajin ya kama, ta dama, lokacin ya warke, ya fara buga kwallon da sandar guragu, ya ce, abin ya ba shi takaici, domin ba abu ne mai sauki ba.

Tun yana dan shekara goma ne Manchester City ta gano shi, kuma ta dauke shi tana renonsa.

Tregaskiss wanda yanzu yake da shekara 22, ya ce, a yanzu yana yin abin da yake kauna, wato taka leda, a kungiyar Manchester City ta guragu.