Kungiyoyin China na son Andy Carroll

Andy Carroll Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Dan wasan West Ham na gaba Andy Carroll ya yi wa Ingila wasa sau tara

Manyan kungiyoyin kwallon kafa na China sun yi tururuwar zawarcin dan wasan West Ham Andy Carroll, lokacin da suka zo farautar 'yan wasan Premier a bana, in ji kocin kungiyar Slaven Bilic.

Sai dai kuma kocin dan kasar Crotia ya ce, ba ta yadda West Ham za ta yarda ta sayar da dan wasan mai shekara 28 a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasan ta watan Janairu.

Tsohon dan wasan gaban na Newcastle da Liverpool ya ci kwallo shida a wasa 12 na Premier da ya yi wa West Ham din a bana duk da raunin da ya yi ta fama da shi.

Bilic ya ce Carroll na daya daga cikin fitattun 'yan wasansu kuma suna son ya ci gaba da zama da su.