Kocin Nigeria ya gayyaci Issac Success

Dan wasan gaba na Watford Isaac Success Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Isaac Success ya yi wa Najeriya wasa a matakin 'yan kasa da shekara 17 da kasa da 20 da kuma kasa da 23

Kocin Najeriya Gernot Rohr ya gayyaci dan wasan Watford Isaac Success tare da wasu 'yan wasan biyar da ba su taba buga wa Super Eagles wasa ba domin taka wa kasarsu leda, a wasan sada zumunta da za su yi da Senegal da Burkina Faso a London a karshen watan nan.

Sauran 'yan wasan da ba su taba sanya jesin Najeriyar ba su ne dan wasan baya Chiedozie Awaziem, da Tyronne Ebuehi da Uche Henry Agbo da 'yan gaba Noah Joel Bazee da kuma Victor Osimhen, wanda shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a gasar 'yan kasa da shekara 17 da duniya ta 2015

'Yan wasan na Super Eagles za su kara da na Teranga Lions na Senegal a ranar 23 ga Maris sannan kuma kwana hudu bayan nan su kara da Stallions na kasar Senegal.

Wasannin dai na zuwa ne kafin wasan da Najeriyar za ta fafata da Afirka ta Kudu, a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin zakarun Afirka ta 2019, a watan Mayu.

Najeriya dai ta yi nasarar sau takwas a wasanninta da ta taka da Senegal sannan kuma sun yi canjaras a wasanni biyar, a inda kuma Senegal ta yi nasara a kanta a wasanni uku.

Sai dai kuma Najeriyar ba ta taba rashin nasara ba a kan Burkina Faso a wasanninsu da suka yi 13.

Najeriya dai wadda ta dauki kofin gasar zakarun na Afirka har karo uku, ba ta samu cancantar shiga gasar ba a gasar guda da suka gabata.