Kofin Duniya : Sai mai katin sheda na musamman ne zai shiga kallo a Rasha

Wani dan kungiyar Orel Butchers ta Rasha, wadanda ke tayar da rikici a filin wasan kwallon kafa Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Wani dan kungiyar Orel Butchers ta Rasha da ke tayar da hankali a filin wasan kwallon kafa da BBC ta yi hira da shi

Duk dan kallon da zai halarci gasar cin Kofin Duniya ta 2018 da gasar Kofin Zakarun Nahiyoyi a bazara mai zuwa a Rasha zai bukaci wani katin sheda na musamman, a wani mataki na yaki da masu tayar da hankali a filayen kallon wasan kwallon kafa.

Hukumomin Rasha za su samar da katin na musamman, wanda 'yan kallo za su gabatar kafin su samu shiga filin wasa, kuma za su iya amfani da shi a matsayin takardar izinin shiga kasar wato biza.

A lokacin gasar cin Kofin kwallon kafa na kasashen Turai na 2016, an samu mummunan tashin hankali tsakanin magoya bayan Rasha da na Ingila a birnin Marseille.

Sannan wani shirin talabijin na BBC da aka nuna a watan da ya wuce, ya nuna cewa wasu sun shirya tayar da rikici a lokacin gasar cin Kofin Duniya na shekara mai zuwa.

Uefa ta ci tarar Rasha tare da yi mata hukuncin hana ta zuwa gasar cin kofin kasashen Turai, wanda aka dage amma idan ta sake aikata wani laifi za a aiwatar da hukuncin, saboda abin da ya faru a gasar ta 2016.

A watan Yuni ne za a fara gasar cin kofin Zakarun Nahiyoyin, kuma za a yi gasar ne a filayen wasa hudu daga cikin birane 11 da za su karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya.

Gasar Zakarun za ta kunshi kasashe tawagar kasashe takwas, da ta hada da kasar da ke karbar bakunci da kuma Zakarun Kofin Duniya Jamus.

A ranar Alhamis ne daraktan gasar wasanni ta Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Colin Smith ya ziyarci Rasha.