Tennis: Murray ya kai wasan kusa da karshe a Dubai

Andy Murray Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Murray yana gasarsa ta farko ne tun bayan da aka fitar da shi a zagaye na hudu na gasar Australian Open a Janairu

Lamba daya a fagen wasan tennis a duniya Andy Murray na Birtaniya ya kai wasan kusa da karshe bayan da ya doke Philipp Kohlschreiber a gasar Dubai.

Murray ya yi nasarar fitar da Bajamushen ne bayan da suka yi kusan kan-kan-kan da farko, inda cikin minti 30 na karshen wasan ya yi galaba da ci 6-7, 7-6, 6-1.

Dan Birtaniyan wanda ya tsira da kyar kuma a gaba zai fuskanci Lucas Pouille ko kuma wanda ya fitar da Roger Federer, Evgeny Donskoy a wasan kusa da karshe, ya ce bai taba yin wasan da ya yi kan-kan-kan irin wannan ba.

Fernando Verdasco da Robin Haase ne za su fafata a daya wasan na dab da na kusa da karshe na gasar ta Dubai