Man United ta barar da damarta - Jose Mourinho

Zlatan Hakkin mallakar hoto Reuters

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce kasa lashe wasan da suka tashi 1-1 da Bournemouth shi ne ya fi daminsa ba wai abubuwan da suka faru a karawar ba.

Mun zubar da damarmu, saboda mun samu damar zura kwallaye hudu ko biyar a zagayen farko na wasan, in ji Mourinho.

Wannan sakamako ya sa United na mataki na shida - matsayin da take tun farkon watan Disamba.

Dan wasan Bournemouth Tyrone Mings ya fado a kan Ibrahimovic na United, amma daga baya ya ce "ba dagangan" ya yi hakan ba.

Ba a jima ba ne kuma Ibrahimovic ya daki Mings da gwiwar hannunsa.

"Shi ne ya kawo kansa jikina," in ji tsohon dan wasan na Sweden, mai shekara 35.

Akwai yiwuwar duka 'yan wasan biyu ka iya fuskantar tuhuma daga hukumar FA idan alkalin wasa Kevin Friend ya ce bai ga lokacin da lamuran suka faru ba.

Labarai masu alaka