Kofin Afirka: Senegal ta doke Kamaru 2-0

Krepin Diatta Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Krepin Diatta lokacin da ya jefa kwallo ta biyu a ragar Kamaru

Senegal ta kai wasan kusa da karshe na gasar cin Kofin kasashen Afirka 'yan kasa da shekara 20, bayan ta doke Kamaru da ci 2-0, a gasar da ake yi a Zambia.

Dan wasan Senegal Niane I. Shi ne ya fara cin kwallo ana shirin tafiya hutun rabin lokaci.

Sannan kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokacin Diatta ya kara ta biyu a minti na 48.

Wasan wanda shi ne na karshe a rukuni na biyu (Group B), na gasar ya sa Senegal ta zama ta daya a rukunin da maki 7 a wasa 3, yayin da Kamaru ta kare a ta 3 da maki 4.

Senegal wadda ba a doke ba a gasar, za ta fafata da Guinea, wadda ta zo ta biyu a rukuni na daya (Group A), da maki 4, a ranar Alhamis 9 ga watan Maris.

A daya wasan rukunin da aka yi tun da farko a yau Lahadi, Afirka ta Kudu ta doke Sudan da ci 3-1.

Hakan ya sa Afrika ta Kudun ta zama ta 2 da maki 6, a wasa 3, yayin da Sudan ta zama ta karshe, ta 4 kenan da maki 1.

Yanzu Afirka ta Kudu za ta hadu da mai masaukin baki, Zambia, wadda ta zo ta daya a rukuni na farko (Group A), da maki 9, a daya wasan kusa da karshe na gasar, a ranar Laraba 8 ga watan Maris.

Dukkanin kasashen hudu da za su fafata a wasannin kusa da karshen sun samu gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya na 'yan kasa da shekara 20 da za a yi a Koriya ta Kudu a watan Mayu na wannan shekara.