Tottenham ta kara matsar Chelsea, da cin Everton 3-2

Harry Kane Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harry Kane ya ci kwallonsa ta 13 a shekarar 2017

Tottenham ta biyu a tebur, ta kara rage ratar da ke tsakaninta da jagorar Premier Chelsea zuwa maki bakwai, bayan a gidanta ta doke Everton 3-2.

Harry Kane mai shekara 23 shi ne ya ci kwallo biyu daga ciki, wanda hakan ya sa, ya zama dan wasan da ya fi cin kwallo a gasar ta Ingila, inda yake da 19, kuma jumulla ya ci kwallo 14, gaba daya a shekaran nan ta 2017, in an hada da sauran gasar kofuna.

Minti 20 da shiga fili ne ya fara daga raga, lokacin da ya sheko wata kwallo daga tazarar kafa 60, wadda mai tsaron ragar bakin Joel Robles, dan Spaniya, ya kasa tare ta.

Dan kwallon gaban na Ingila ya ci ta biyu ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, a minti na 56.

Romelu Lukaku ya rama wa Everton kwallo daya a minti na 81, wanda wannan shi ne hari na biyu da bakin suka kai ragar Tottenham.

A cikin karin lokacin tashi ne, minti biyu a kan 90 na ka'ida, sai Dele Alli ya kara jefa kwallo ta uku ragar Everton.

To amma bakin ba su karaya ba, domin minti daya tsakani, ya rage dakika kadan a tashi, sai Enner Valencia wanda ya shigo daga baya, ya keta wani tarkon satar gida da 'yan bayan Tottenham suka shirya, ya sheka musu kwallo ta biyu kuma ta karshe a raga.

Wannan ita ce nasara ta 16 da Tottenham ta yi a gasar ta Premier a bana, yayin da Everton ta ci gaba da zama ta bakwai a tebur da maki 44, a wasa 27.

Sai dai Chelsea za ta iya sake bayar da ratar maki goma tsakaninta da ta biyun, idan ta yi nasarar doke West Ham a haduwarsu ranar Litinin.

Tarihin da wasan ya kafa

-Kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya yi nasara a karo na dari a wasan kwallon kafa da yake jagoranta a Ingila,a matsayin koci, inda ya yi nasara sau 77 a wasa 15 da ya yi da Tottenham, yayin da ya yi nasara 23 a wasa 60 da ya jagoranci Southampton.

-Tottenham ta yi nasara a gida sau tara a jere a wasan Premier; abin da ba ta taba yi ba a gasar.

- A karon farko tun kakar 1964-65 ba a doke Tottenham a manyan wasanninta na lig 14 na farko a gida ba.

-Romelu Lukaku ya zama dan wasan da ya fi ci wa Everton kwallo a tarihin gasar Premier, inda ya ke da kwallo 61.

-Lukaku wasan ya ci kwallo 18 a Premier

-Lukaku ya ci kwallo18 a wasannin Premier a bana, inda ya zo daidai da yawan kwallon da ya ci a bara, kwallo 18 a wasa 37.

- Tun da aka fara kakar bara ba dan wasan tsakiya da ya ci kwallo a Premier fiye da Dele Alli, mai 23.

-Kevin Mirallas ya ba wa Lukaku kwallo ya ci a Premier fiye da kowane dan wasa, inda ya ba shi har sau goma.

-Harry Kane ya ci kwallon Premier a gida guda 14 a bana, wanda ba wani dan wasan Tottenham da ya taba yin haka a kakar Premier daya.

Wasannin gaba na kungiyoyin biyu

Tottenham a gidanta za ta hadu da Millwall, a wasan dab da na kusa da karshe na Kofin FA, ranar Lahadi, kafin kuma su sake dawowa wasan Premier wata Lahadin a gida da Southampton.

A gida Everton za ta karbi bakuncin West Brom a gasar Premier, ranar Asabar mai zuwa.