Serie A: Juventus ta yi canjaras da Udinese

Leonardo Bonucci lokacin da yake cin Udinese Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Leonardo Bonucci ya tabbatar ba a doke Juventus ba, inda ta yi canjaras na farko a Serie A tun Fabrairun 2016

Juventus ta bayar da ratar maki takwas a gasar Serie A ta Italiya, inda take da maki 67, duk da canjaras da ta yi a gidan Udinese.

Duvan Zapata ne ya fara ci wa masu masaukin bakin kwallo a minti na 37, bayan ya keta Leonardo Bonucci, ya sheka kwallon tsakanin kafafuwan Gianluigi Buffon.

Bonucci ne ya rama wa bakin da ka, daga bugun tazara da Paulo Dybala ya yi a minti na 60, wanda wannan shi ne karo na farko da Juventus ta yi canjaras a gasar lig din, a sama da shekara daya, ko da yake Udinese ta kusa yin nasara lokacin da Danilo ya buga wata kwallo da ka ta bugi sandar raga.

Roma ce ta biyu da maki 59, bayan wasan na mako na 27, yayin da napoli ke matsayi na uku da maki 57, inda Pescara take ta karshe (20) da maki 12.

A sauran wasannin na La Liga na ranar Lahadin Inter Milan ta doke Cagliari 5-1 inda Ivan Perisic ya daga raga sau biyu.

Andrea Belotti ya ci kwallo uku a minti 17 na karshe na wasansu, wanda Torino ta farfado daga baya ta doke tsohuwar kungiyarsa Palermo 3-1.

Minti bakwai da dakika 15 tsakanin kwallaye ukun da ya ci, ya sa ya zama dan wasan ya ci kwallo uku mafi sauri a gasar Serie A, tun bayan tarihin da Andriy Shevchenko ya kafa, lokacin da AC Milan ta ci Perugia a shekara ta 2000.

Ita kuwa Genoa a cikin minti biyu na karshen wasansu ta doke Empoli 2-0, yayin da Atalanta ta yi canjaras ba ci 0-0, a karonta da Fiorentina, kamar yadda Crotone da Sassuolo suka tashi ba ci.