Aguero ya kara yi wa Man City rana, ta ci Sunderland 2-0

Sergio Aguero na jefa kwallo a ragar Sunderland Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Karo hudu kenan Aguero ya ci kwallo a duk zuwansa gidan Sunderland

Sergio Aguero ya ci kwallonsa ta biyar a wasa uku, ya taimaka wa Manchester City ta koma ta uku, abin da ya kara dankwafar da Sunderland a karshen teburin Premier.

Masu masaukin bakin sun kare gidansu sosai, kafin Man City din su mayar da martani cikin gaggawa na wani hari, inda Sergio Aguero ya kwarara kwallon da Raheem Sterling ta tura masa, a raga, a minti na 42.

Daga nan ne kuma sai bakin suka tashi tsaye, inda David Silva ya ba wa Leroy Sane wata kwallo, wadda Bajamushen bai yi wata-wata ba sai kawai ya kwararata a raga, a minti na 59, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Can a kusan karshen wasan Jermain Defoe ya daga ragar Man City, a wani hari na bazata da Sunderland din suka kai, amma, aka ce ya yi satar gida.

Ana ganin Pep Guardiola zai yi fatan wannan nasara, tare da ta Tottenham wadda ke matsayi na biyu, za su sa hankalin Chelsean Antonio Conte ya fara tashi.

Wannan ita ce nasara ta hudu da Manchester City ta yi a jere a Premier, kuma kungiyar na kara tashi tsaye, wanda hakan zai kara sa abokan hamayyarta fargaba, a lokacin da za ta yi kwantan wasanta da Stoke ranar Laraba.

Sai dai kuma hankalinta ya rabu a gasa uku, inda da wannan nasara ta fara fafatawa a wasa biyar a cikin kwanaki 15, wadanda suka hada da, karo na biyu a Monaco, na zagayen kungiyoyi 16, na Kofin Zakarun Turai, da kuma wasan dab da na kusa da karshe na Kofin FA a gidan Middlesbrough.