Bayer Leverkusen ta kori kociyanta Roger Schmidt

Roger Schmidt Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bisa jagorancin Schmidt, Bayer Leverkusen ta doke Tottenham a Wembley a gasar Zakarun Turai

Bayer Leverkusen ta kori kociyanta Roger Schmidt bayan da Borussia Dortmund ta casa su da ci 6-2 a ranar Asabar.

Rashin nasarar da kungiyar ta yi a wasanta hudu daga cikin shida na Bundesliga ya sa ta yi kasa zuwa matsayi na tara a gasar.

Ana daukar Schmidt, mai shekara 49, a matsayin daya daga cikin kwararrun kocin babbar gasar ta Jamus, sannan ana ganinsa a matsayin wanda zai iya maye gurbin Arsene Wenger, idan Bafaranshen ya bar Arsenal.

Har yanzu kungiyar ta Jamus tana cikin gasar cin Kofin Zakarun Turai, amma kuma suna bayan Atletico Madrid wadda ta ci su 4-2, a wasansu na farko na zagayen kungiyoyi 16.

Darektan wasan kungiyar, Rudi Voller ya ce, ya yi amanna Roger Schmidt kwararren kociya ne, ba tantama akan hakan, amma dole ne su dauki mataki a yanzu, in dai har ba so suke su kasa cimma burinsu ba.