Atletico Madrid ta koma ta hudu

Fernando Torres a cikin 'yan kallo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Atletico Madrid ba ta ji rashin Fernando Torres wanda ya kalli wasan a cikin 'yan kallo ba

Atletico Madrid ta sake komawa gurbin samun zuwa gasar Kofin Zakarun Turai bayan da ta lallasa Valencia a gasar La Liga.

Dan wasansu na gaba Fernando Torres ya kalli wasan ne a cikin 'yan kallo, kwana biyu bayan an sallame shi daga asibiti sakamakon raunin da ya ji a ka a lokacin wasan da suka yi na karshe.

Antoine Griezmann ne ya fara ci, sai Kevin Gameiro ya kara ta biyu, sanna kuma Griezmann din ya kara ta uku can a karshen wasan.

Yanzu Atletico na matsayi na hudu da bambancin maki daya da ta biyar, Real Sociedad, amma kuma maki shida ne tsakaninta da Sevilla ta uku.