Wenger ya karyata rigimar Sanchez da 'yan wasan Arsenal

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sanchez ya ci wa Arsenal kwallo 17 ya taimaka aka ci tara a bana

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce rahotannin da aka bayar cewa Alexis Sanchez ya yi rigima da wasu 'yan wasan Arsenal a filin atisaye karya ce tsagwaronta.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Sanchez ya yi cacar-baki da wasu abokan wasansa, bayan da ya bar fili ana tsakiyar atisaye kafin wasan da Liverpool ta doke su 3-1 ranar Asabar.

Wasu daga cikin 'yan wasan sun tunkare shi da maganganu cikin fushi a lokacin da suka je dakin sauya kaya, yayin atisayen

Wenger ya ce , shi dai ban san wannan abu ya faru ba.

Ba a fara wasan da Sanchez ba, amma ya shigo a kashi na biyu na wasan na Anfield inda ya taimaka wa kungiyar ya ci daya.

Wenger ya ce dan wasa ne mai kishi wanda wani lokaci yake da wuyar sha'ani, to amma kuma wannan abu ne da ke faruwa sau da dama a kowace kungiya.

Kocin na Arsenal yana wannan magana ne, kafin wasansu na biyu na Kofin Zakarun Turai na ranar Talata, na zagayen kungiyoyi 16, a gida da Bayern Munich wadda ta ci su 5-1.

Da aka tambayi kocin akan dangantakarsa da Sanchez, sai Bafaranshen ya ce, ba wata matsala, suna jituwa kamar yadda suke yi da kowane dan wasa.

Sanchez ya taimaka wajen kwallo 26 da Arsenal ta ci a bana, inda ya ci 17 kuma ya bayar aka ci tara.

Tsohon dan wasan Arsenal na gaba Ian Wright ya ce da shi ne dan wasan na Chile (Sanchez) da zai bar kungiyar ne kawai.

To amma Wenger ya ce, Alexis Sanchez yana da sauran wata 15 a kwantiraginsa , saboda haka duk wani mataki yana hannun Arsenal ne ba wani mutum ba.